A yau Litinin ministan harkokin wajen kasar Jamus ya fada cewa, gwamnatin Jamus za ta hana wasu 'yan kasar Saudiyya su 18, shiga yankin nan na Schengen wato wasu rukunin kasashen tarayyar Turai 26, wanda ba sai da fasfot ake shigarsu ba, saboda ana zargin su da alaka da kisan gillar da aka yi wa dan jaridar kasar Saudiya Jamal Khashoggi.
Ministan harakokin wajen, Heiok Maas ya ce sai da ya tuntubi kasashen Faransa da Birtaniya kafin ya fito da wannan dokar.
Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce an yi masa cikakken bayani akan faifan rediyon da aka nada yayin da ake kashe dan jaridar nan a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya, dake Santanbul a watan da ya gabata.
Aamma ya ce bashi da niyyar ya saurari kaset din saboda tashin hankalin da yake cikinsa.
Shugaba Trump ya fada a ranar Asabar cewa a ranar Talata mai zuwa, gwamnatin Amurka zata bada cikakken bayanin abun da ta gano na kisan da aka yiwa Khashoggi a ranar 2 ga watan Oktoba da ta gabata.