Kokarin shawo kan ‘yan majalisar dokokin Burtaniyya da Firayin minista Theresa May ke yi akan amincewa da yarjejeniyar fitar kasar daga Tarayyar Turai ya fuskanci tangarda yau Alhamis bayanda sakataren harkokin kasar akan ficewar Burtaniyya daga tarayyar Turai, Dominic Raab yayi murabus.
Raab ya ki ya amincewa da wasu muhimman tanade-tanade dake cikin yarjejeniyar wacce ke neman a kafa wata hukumar kwastan ta hadin-guiwa ta kasashen, wacce zata maye gurbin ayyukan da ake gudanarwa akan iyakokin dake tsakanin kasar Ireland ta Arewa, wadda bata cikin tarayyar Kasashen Turai da ake kira EU a takaice, da kuma kasar Ireland, wacce tana cikin tarayyar.
A karkashin shawarar da aka gabatar, ana son wannan sabuwar Hukuma ta yi aiki ne yayinda Burtaniyya da EU ke kokarin dinke barakar dake tsakaninsu a kan maganar harakokin cinikayya.
Facebook Forum