Mai gabatar da karar gwamnatin Saudiyya ya bukaci a yankewa mutane 5 da ake zargi da kisan dan jaridar kasar, Jamal Khashoggi hukuncin kisa.
Ranar 2 ga watan Oktoban da ya gabata ne aka kashe dan jaridar mai yawan sukar yariman Saudiyya Mohammed bin Salman a jaridar Washington Post, bayan da ya ziyarci karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Istanbul a kasar Turkiyya.
Mai magana da yawun ofishin mai gabatar da karar ya fada yau Alhamis cewa, an ba Khashoggi wata allura mai illa sosai kuma bayan da ya mutu an daddatse jikinsa.
Jami’an Saudiyya sun bada bayanai dabam dabam tun bayan da Khashoggi ya bace, ciki har da cewa Khashoggi ya fita daga Ofishin da kansa, suka kuma ce ya mutu ne bayan wani fada da yayi, sannan suka ce an kashe shi ne a yayinda aka yi kokarin kama shi a matsayin wani mara gaskiya.
Facebook Forum