Hukumomin kasar Saudiyya na hukunta duk wata kasar da aka samu ta bar Alhazanta mata masu juna biyu sun tafi aikin hajjin. Mukaddashin sakataren hukumar jin dadin alhazan jihar Neja, Alhaji Umar Makum, ya tabbatar da cewa yanzu haka sun jinkirta tafiyar matan su biyar har sai zuwa shekara mai zuwa, bayan da likitoci suka tabbatar da cewa suna dauke da juna biyu.
Kwamandan agaji da ke taimakawa Alhazan a sansanin alhazan jihar Neja, Awwal Musa Gulma, yace wannan matsala babba ce bisa la’akari da dokokin kasar Saudiya. Saboda an shawa yin irin wadannan tsare tsare sai dai mutane kan yi burus da al’amuran da suka shafi doka.
Ranar 4 ga watan gobe ake sa ran kasar Saudiyya zata rufe filayen jiragen saman Jidda da Madina, amma hukumomin Najeriya sun bayar da tabbacin cewa zasu kammala jigilar alhazansu kimanin 76,000 kafin lokacin.
Saurari cikakken rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5