An gwabza fada a bangarori da dama a Yankin Gabas ta Tsakiya a ranar Alhamis, inda aka kashe akalla mutum 16.
Hukumomi sun ce makamai masu linzami da aka harbo daga Lebanon sun kashe mutum biyar a arewacin Isra’ila, ciki har da wani manomi da wasu ma’aikata ‘yan kasashen wajen hudu.
Lebanon ta ce hare-haren Isira’ila sun kashe akalla mutum takwas, ciki har da ma’aikatan lafiya shida a kudancin kasar.
A halin da ake ciki, jami’an Falasdinawa sun ce wani harin Isra’ila a Yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye ya kashe mutum uku.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kuma kai hari kan wuraren ajiyar makamai da sansanoni a Syria, inda ta yi ikirarin cewa kungiyar mayakan a baya-bayan nan ta fara ajiye makamai a kan iyakar Syria da Lebanon, domin yin fasakaurin su zuwa Lebanon.
Isra’ila ta ba da sanarwar ficewa ta gargadin ga mazauna Baalbek a gabashin Lebanon a rana ta biyu a jere.