A yau aka gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Legas kuma zaben ya tafi dai dai yadda aka tsara a wasu yankuna na birnin Legas,inda ba a samu ambaliyar ruwa ba.
Rahotani na nuni da cewa jama’a sun fito sosai domin jefa kuri’arsu, amma akwai rahotani dake cewa ba a samu fitowar mutane da dama ba a yankunan da aka samu ambaliyar ruwa sama kamr da bakin kwarya ba.
Bincike ya nuna cewa ba a kai kayan zaben yakunan da aka samu ambaliyar ruwa ba koda yake ita kanta hedkwatar hukumar zabe ta jihar Legas, a daya daga cikin yankunan da aka samu ambaliyar ruwan sama ne ana ganin cewa batun ambaliyar ruwa shine ya jawo rashin kai kayan zabe.
Wurare kamar su Ikoyi da Yaba bangaren dake kusa da ruwa su fuskanci ambaliyar ruwa wanda ya jawo tsaiko ga zaben kananan a birni na Legas.
A wasu wurare sai kusa karfe uku aka fara zaben a maimakon karfe tara na safe kamar yadda aka saba gudanar da zabe kuma da ana sa ran rufe rufunar zaben ne da karfe uku, na rana.
Your browser doesn’t support HTML5