An Gudanar Da Taron Wayar Da Kan Al’umma Kan Zabiya

Kungiyar fafutukar kare hakkin Zabiya ta yi taro na musamman don jan hankalin mutane cewa haihuwar Zabiya ba wata illa bace ga al’umma.

Taron dai ya sami halartar masana da jami’an shari’a don kara fayyacewa mutane halin wariya da Zabiya ke fuskanta wajen rashin daukarsu aiki ko kyamar mu’amula da su.

Babban alkalin kotun birnin tarayya Abuja, Justice Usman Bello, ya halarci taron da kuma nuna takaicin yadda aka hana wani Zabiya gurbin aiki. Inda ya ce kowanne mutum Allah ne ya halicce shi kuma babu wani dalilin da zai sa ayiwa wani kallon kaskanci ko kyama ba.

Daya daga cikin dinbin Zabiyan da suka halarci taron, Donal Tamfi, ya koka ga yadda yace al’umma na nuna musu wariya. Inda yace suna yin iyaka kokarinsu domin ganin al’umma ta daina nuna musu wariya.

Domin karin bayani saurari rahotan Saleh Shehu Ashaka.

Your browser doesn’t support HTML5

An Gudanar Da Taron Wayar Da Kan Al’umma Kan Zabiya - 2'22"