Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kanu: “’Yan Kabilar Igbo Sun Tayar Da Kura”


Nnamdi Kanu Shugaban IPOB
Nnamdi Kanu Shugaban IPOB

Rikicin da ake yi kan fafatukar awaren 'yan kabilar Igbo da Nnamdi Kanu ke jagoranta ya dau wani sabon salo, bayan da wasu magoya bayan Kanun su ka shiga far ma mutane tun bayan da yinkurinsu na yin arangama da sojoji ya ci tura.

Rahotanni daga garin Aba na jahar Abia, na nuna cewa ‘yan kungiyar IPOB masu ra’ayin dan awaren nan Nnamdi Kanu, sun shirya gangami wanda ya kai ga kone-kone da jiye-jiyen raunuka musammam ma ga wasu ‘yan arewacin kasar mazauna kudu maso gabashin kasar da ma wasu da ke kudu maso kudancin kasar.

‘Yan kabilar ta Igbo sun yi gangami ne daga Aba don yin tattaki zuwa garin Ummahia duk da ke jahar Abia don kai ziyarar nuna goyon bayan ga Shugaban kungiyar ta IPOB Nnamdi Kanu, lokacin da wasu daga cikin masu gangamin su ka far ma wasu ‘yan arewacin Najeriya a kasuwar ‘yan albasa da ke Aba a jahar ta Abia.

Shugaban kasuwar ‘Yan Albasan Alhaji Salihu Danwanzam ya ce tun da misalin karfe 9 na safe matasan su ka fara shirin tafiya Ummahia wai za su je su fuskanci sojoji. Ya ce da aka hana su shiga, garin sai su ka dawo su ka far ma mutane, akasari ‘yan arewa. Wani mai suna Lawali ya bayyana cewa an sara masa hannu, kodayake ba ssu dake shi ba. Wani dattijo mai suna Alhaji Barkum, dan asalin Karamar Hukumar Bunkure, jahar Kano ya ce an kai mutane wajen hudu zuwa biyar asibiti.

Ga wakilinmu Lamido Abubakar da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG