Gwamnatin jihar Kaduna ta ce kimanin matasa 3000 ne zasu samu ayyukan yi a sabon kamfanin kaji na Olam da shugaba Buhari ya kaddamar yau a Kaduna.
Manoma zasu samu sabuwar kasuwar sayar da masara da waken soya da kaji da abincin dabbobi.
Yayinda yake jawabi a wurin kaddamar da kamfanin wanda Shugaba Muhammad Buhari yayi a karamar hukumar Chukun ta jihar Kaduna gwamnan jihar Nasiru El-Rufai ya ce gwamnatin jihar zata anfana matuka da kamfanin.
Manoma zasu anfana saboda kowace shekara kamfanin zai bukaci buhun masara miliyan biyu da buhun waken soya miliyan daya. Kamfanin zai kaowa ayyuka ma mutane da dama baicin matasa.
Gwamnatin Kaduna ce ta biya kusan Nera miliyan 500 a matsayin kudin diya wa masu filayen da aka kafa kamfanin domin kamfanin ya yi anfani da kudinsa wajen yin aikin. A cewar gwamnan daga harajji da sauran faidoji da zasu zo wa jihar zata mayar da kudin da ta kashe.
Ministan wasanni da matasan Najeriya ma yana wurin kaddamar da kamfanin. Yace yau gwamnan Kaduna bai rushe gidaje ba amma ya rushe talauci.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.
Facebook Forum