Shugabannin kungiyoyin ci gaban matasa daga kasashen Afirka kimanin 12 na gudanar da taro a jamhuriyar Nijar, domin tattauna wa akan matsalolin dake jefa matasa cikin ayyukan ta'addanci, da rungumar tsatsauran ra'ayi.
Taron na da nufin gabatar wa gwamnatoci shawarwarin da zasu taimaka a samar wa matasa kwararan madogara, da za ta kare su daga kwadayin zuwa cirani ko shiga aiyukan tayarda zaune tsaye.
A kalla matasa sama da 100 daga sassan Afirka ne suka halartci wannan taro, don samun nazarin ainihin matsalolin da ke cusawa matasa mugun tunanin dake jefa wasu afkawa cikin ayyukan ta’addanci, kuma wasu ke yanke shawarar zuwa cirani ta haramtaciyar hanya, ba tare da la’akari da irin hadarin da suke jefa rayuwarsu ciki ba.
Mohamed Sidi, mamba ne a majalisar ci gaban matasan Nijar CNJ, a hirar su da wakilin Muryar Amurka, yayi bayanin hanyoyin da za'a samar don matasa su shiga, mai makon hanyar banza.
Mataimakin sakataren kungiyar matasan Afirka Beining Ahmed, mai wakiltar kasar Ghana ya bayyana cewa akwai bukatar kawo karshen tsarin da ‘yan mulkin mallaka suka shimfida a kasashen Afirka. Ya bada misalin cewa Nijar kasa ce da ta wuce duk wasu kasashen duniya akan maganar ma’adanan Uranium. Amma matasan Nijar na wa ne ke morar wannan arzikin?
Yace gaba daya Faransa ake kai komai, to ba ma bukatar wannan tsari. So muke a kafa kamfanoni anan, kuma a baiwa matasa dama su shiga a dama da su.
Ya kara da cewa idan kaje Ghana ko Najeriya zaka ga kamfanonin ketare ne suka mamaye dukkan manyan harkoki a wadanan kasashe, ba ma jin dadin haka saboda haka muke bukatar gwamnatoci su dauki matakai.
Shigar matasa cikin harkokin siyasa har zuwa matakin fada aji, wani abu ne da shugaban majalisar matasan Najeriya Bello Bala Shagari, ke ganin zai taimaka wajen kawo karshen wasu matsaloli da ake fuskanta a kasashen Afirka.
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta gargadi mahalarta taron su shirya makamanatan wannan taron a kasashen da suka fito, don isar da sakon dake kunshe cikin shawarwarin da aka tsayar.
A yammacin yau ake kammala wannan taro dake hangen karfafa zaman lafiya ta hanyar samarwa matasa kwararar madogara.
A saurari cikakken rahoton wakilin muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5