‘Yancin kai da kawo daga wannan kasa zuwa waccan ko daga wannan gari zuwa wancan na daga cikin mahimman ‘yancin da kasashen duniya suka yi amanna akansu ta hanyar yarjeniyoyin da suka sakawa hannu.
To sai dai rashin mallakar takardun da suka shata tsarin shigi da ficin kasa da kasa wata babbar matsala ce da kan jefa ‘yan cirani cikin halin cin zarafi, yayinda kafafen yada labarai kan yi amfani da kalaman da ba su dace ba akan irin wadanan mutane dake neman mafakar wasu matsalolin da suke fuskanta a yankunan da suka fito.
Saboda haka kungiyar AJSEM da UNESCO suka shirya wannan taro da nufin ankarar da ‘yan jarida akan wannan batu a cewar kakakin kungiyar ta AJSEM Tsahirou Abdou.
Wakilin UNESCO a wurin wannan taro Ousman Djibo ya fayyace burin da kungiyar ta sa gaba a karkashin irin wannan zama da ‘yan jarida.
Ya ce makasudun wannan taro shine su karawa juna sani tsakaninsu da ‘yan jarida domin baiwa al’uma musamman matasa labarai na hakika akan batutuwan da suka shafi zuwa cirani kamar illolin dake tattare da zuwa cirani ta barauniyar hanya da kuma maganar mutunta ‘yancin ‘yan cirani yayinda za su nemi hadin kan shugabanin kafafen labarai don ganin sun matsa kaimi wajen gabatar da shirye-shiryen fadakarwa akan batun zuwa cirani.
Kungiyar AJSEM ta bayyana shirin ci gaba da shirya irin wannan taro domin ‘yan jarida na dukkan jihohin Nijar don ganin sun shiga wannan sabuwar tafiya ta neman kare ‘yancin bakin haure.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5