An Gudanar Da Taron Jaddada Zaman Lafiya Da Tsaro a Filato

Wadanda suka halarci taron neman zaman lafiya da tsaro da tattalin arziki

Gwamnatin jihar Filato ta ce ta fito da wasu tsare-tsare na tallafawa matasa mata da maza da sauran masu karamin karfi ta yadda za su samu sana'o'in yi domin dogaro da kai da inganta zaman lafiya a jihar.

An gudanar da taron masu ruwa da tsaki da hukumar inganta zaman lafiya ta jihar tare da hukumar tsaro da hukumar ba da tallafi ga masu kananan masana'antu suka shirya a Jos domin tattauna hanyoyin inganta tsaro da rayuwar al'umma.

Taron neman zaman lafiya tasaro da tattalin arziki

Sakataren gwamnatin jihar Rufus Bature ya ce gwamnati ta kirkiro tsare-tsaren samar da aikin yi wa al'ummarta. Ya kuma ce yau a jihar Filato an samu zaman lafiya da fatan zai zama na dindindin.

Shugaban hukumar samar da tsaro ta jihar Janar Stephen Gua'ar ya ce idan jama'a na da aikin yi ya yi imani tsaro zai tabbata ya na jaddada cewa idan mutum na da abin yi ba zai je neman fitina ba.

Taron neman zaman lafiya tasaro da tattalin arziki

Shi ma shugaban hukumar inganta zaman lafiya Joseph Lemang ya ce makasudin taron shi ne su hada gwiwa da masu ruwa da tsaki wajen samun zaman lafiya mai dorewa.

Shi ko shugaban hukumar yaki da talauci a jihar Haruna Gutap ya ce akwai tsare-tsare da suka yi ta yadda al'umma da suka yi kungiyoyi za su samu gajiyar tallafin.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Gudanar Da Taron Jaddada Zaman Lafiya Da Tsaro a Filato - 3' 57"