A cigaba da gano wasu abubuwan tayar da hankali da kungiyar IS ta gudu ta bari, a baya bayan nan an gano wasu manyan kaburbura.
WASHINGTON DC —
Yayin da hukumomi a arewa maso gabashin Syria suka sanar da gano wasu sabbin ramuka da aka jibge gawarwakin wadanda fadan yan kungiyar IS ya shafa a birnin Raqqa, iyalan wadanda ‘yan uwansu suka bace a lokacin da kungiyar ke rike da ikon yankin na fatan samun bayanai.
Tawagar ma’aikatan gaggawa, da na ceton rai a arewa maso gabashin Syria, a farkon watan nan suka sanar da cewa sun gano wani babban rami da aka binne mutane a yamma da wajen yankin Farusiya da ke Raqqa, abinda ya sa yawan irin wadannan wuraren da aka gano a wannan shekarar ya kai 5.
Biyo bayan sanarwar da kuma gano gawarwaki 16 daga ramin, iyalan wadanda lamarin ya shafa sun bukaci hukumomi su maida hankali wajen tantance gawarwakin mutanen.