Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Kwamanda a Sojin Amurka Ya Yi Gargadi Kan Sake Dawowar IS


Janar Kenneth Frank McKenzie
Janar Kenneth Frank McKenzie

Babban kwamanda mai kula da ayyukan dakarun sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya ya yi gargadin yiwuwar sake dawowar ayyukan kungiyar IS, muddin al’ummomin kasa-da-kasa basu gaggauta daukar mataki ba.

Janaral Kenneth Frank McKenzie, kwamandan runduna ta tsakiya ya fada a wani dandalin yanar gizo a yau Laraba, cewa “Muna sayawa kan mu matsala nan da shekaru 10 ko 15, aikin zai koma mana kasa. Ya kamata mu gujewa haka.” Bisa ga cewarshi ana bukatar gaggauta daukar matakin wanke kwakwalwa ga tsofaffin magoya bayan kungiyar ta ‘yan ta’adda da suke a sansanonin kasar Syria.

Dakarun kawancen kasa-da-kasa da Amurka ke jagoranta masu yaki da kungiyar IS, sun ayyana samun nasara akan kungiyar ta ‘yan ta’adda a shekarar bara, to amma kuma McKenzie ya ce har yanzu akwai sauran matsaloli da ke bukatar hadin gwiwar kasashe.

Kasashe sun yi kokarin cimma yarjejeniya ta bai daya, akan yadda za’a yi da mayakan kungiyar ta IS da aka kama da kuma iyalansu, inda kasashen da dama suka ki amincewa ‘yan kasarsu da suka fice domin shiga yaki a Iraki da Syriya su sake komawa kasashen na su.

Jami’ai sun ce mummunan yanayin sansanin al-Hol da ke Syria, wanda ya hada mayakan IS da aka kama da kuma dubban mutanen da yaki ya daidaita maza da mata da yara kanana, yana kara uzzura tsattsauran ra’ayi.

Haka kuma an tabbatar da samun kamuwa da cutar COVID-19 na farko a sansanin, wanda ya kara zafafa fargabar cewa cutar na iya yaduwa.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG