An Gano Mutumin Da Ya Tsara Harin bom a Jirgin Daallo Airlines

An aircraft belonging to Daallo Airlines is parked at the Aden Abdulle international airport after making an emergency landing following an explosion inside the plane in Somalia's capital Mogadishu, Feb. 3, 2016.

Jami’an tsaron kasar Somaliya sun ce sun gano mutumin da suke da yakinin shine ya tsara harin bam din da aka dasa da nufin kakkabo jirgin kamfanin Daallo Airlaines a makon da ya gabata.

Wani jami’in da ya yiwa sashen Somali na nan Muryar Amurka bisa sharadin sakaya sunansa, ya bayyana cewa su jami’an sun san ko wanene, kana yana da alaka da wani harin da ‘yan kungiyar Al-Shabaab suka taba kaiwa.

Jami’in yace, shi wannan mutum yana sana’ar sayar da wayoyin hannu ne da tabarau hade da suturun sawa, wanda yake amfani da wannan sana’a wajen badda sawun ayyukan ta’addancin da yake yiwa kungiyar ta Al-Shabaab.

Ya kara da cewa wannan dan mta’addar bai zo hannu ba, don kuwa ya tsere, sai dai an masa ganin karshe ne a wani gari da ake kira Afgoye a makon da ya gabata, inji wannan jami’in tsaro.