Jami’an ‘yan sandan kasar Lebanan sun bayyana cewa sun gano makudan kudade a asusun ajiyar bankin Fatima Othman, mai shekaru 52, da haihuwa, mabaraci kuma mai nakasa da ta rasu a birnin Beirut dake kasar Lebanon.
‘Yan sandan sun gano wannan abin al’ajabi ne a yayin da suke binciken rasuwar Fatima, inda suka sami wasu robobin da take bara da su guda biyu, daya da tsabar kudi da yawansu ya kai dalar Amurka $ 4389, kwatankwacin Naira 1,558075, da kuma takardun shaidar ajiyar banki a daya robar inda suka ga cewar mabaraciyar ta tara kudi dalar Amurka $1,491,866 a wani banki dake kusa da inda take bara.
Mai Magana da yawun jami’an ‘yan sandan birnin Joseph Mussaem, ya bayyana cewa wannan abin al’ajabi ne kwarai, kamar yadda masu bata sadakar abinci da kudi suka rasa abin da zasu ce sabo da mamaki.
Fatima’ da tara makudan kudade sama da dalar Amurka Miliyan daya da dubu dari hudu da tasa’in da daya da dari takwas da sittin da shida.
Fatima, ta kasance wadda labarin ta ya mamaye shafukan sadarwa na yanar gizo inda aka nuna hoton ta da wani sojin kasar yana bata ruwan sha sakamakon matsalar hannuwa da kafafu da take fama da su.