An Gano Gawarwakin Bakin Haure a Libya

Wasu 'yan gudun hijira a birnin Tripoli da ake ceto

Rundunar sojin ruwan Libya ta bayyana cewa ta gano gawarwakin bakin haure 11 tare da tseratar da 263 a yammacin bakin tekun Libya.Bakin hauren sun fito ne daga kasashen Afrika da dama.

Libya dai itace kasar da bakin haure suka fi yawan ratsawa akan hanyar su zuwa turai ta teku. Fiye da mutane 600.000 ne suka tsallaka tekun Bahar Maliya zuwa Italiya a cikin shekaru 4 da suka wuce, wanda mafi yawancin su daga Libya ne.

Cibiyar dake kula da bakin haure Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa ‘yan gudun hijira dubu 18 da 575 ne suka isa kasashen Italiya , Girka da Spain ta hanyar tsallaka kogin na maliya.

A shekarar da ta gabata mutane dubu 3116 ne suka rasa rayukansu a yayin da suke kokarin tsallaka tekun, a cewar kungiyar IOM, dubu 2833 daga Libya suke.