Shekaru kusan hudu ke nan da ‘yan kasar Nijar suka daina jin duriyar jirgin sama safuring boeing 747 da mahukuntan kasar ke anfani dashi.
Rashin ganin jirgin ya sa jama’ar kasar suna shakkun inda yake dalili ke nan da ‘yan adawa suka bukaci gwamnatin kasar ta fitar da jama’a daga duhu.
A bayanan da ya bayar a zauren majalisar dokokin kasar ministan tsaron kasa Kalla Mukhatari ya sanar cewa gangaci ne na ‘yan adawa da suka yi zargin bacewar jirgin. A cewarsa shekaru 40 da suka wuce aka sayi jirgin. Yanzu yana Ingila wurin gyara.
An kiyasta cewa kudin jirgin zai kai kimanin miliyan dari biyar na sefa amma yana bukatar miliyan dubu biyu na sefa domin a yi masa gyaran da yake bukata. To sai dai an gano cewa duniya ta daina yayin irin jirgin saboda haka masana suka shawarci gwamnatin kasar ta yi gwanjonsa.
Hukumomin kasar Nijar sun ce zasu sayar da jirgin ga mai so saboda babu yadda za’a yi dashi a wannan zamanin.
Amma kakakin ‘yan majalisar dokoki na bangaren adawa Sumaila Sanda wanda shi ya bukaci sanin inda jirgin yake na ganin rashin dacewar sayar dashi saboda ya yiwa kasar aiki.
Souley Barma nada karin bayani a rahotonsa
Facebook Forum