Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru Ta Tsare Ma'aikata 16 Kan Zargin Fallasa Sirrin Gwamnati.


Shugaba Paul Biya.
Shugaba Paul Biya.

Cikin wadanda ake tsare da su harda jami'an 'Yansanda uku wadanda suke dakon shari'a kan zargin fallasa umarnin gwamnati data baiwa jami'an tsaro na takaita tafiye-tafiye wasu jami'an gwamnati da ake zargi da sama da fadi da dukiyar al'uma.

A kamaru rahotanni suka ce yanzu ya zama abu na yau da kullum aga takardu ko bayanai na sirrin gwamnati a kafofin sada zumunta. Jawabai na shugaba Paul Biya ga al'umar kasar guda biyu, na baya bayannan, an gansu a kafofin sada zumunta gabannin ma ya gabatar da jawaban. Hukumomi suna daukar matakai na magance aukuwar haka.Kamar yadda Moki Edwin Kindzeka, ya aikowa wannan tasha, yanzu an tsare akalla jami'an gwamnati su 16 kan zargin fallasa sirri ko bayanan gwamnati tun shigar wannan shekara.

A cikin watan Maris da ya gabata, wasu bayanai na sirri, ya fara yawo a kafofin sada zumunta a kasar, inda a ciki, gwamnati ta baiwa jami'an tsaro umarnin takaita tafiye tafiyen wasu manyan jami'an gwamnati su kusan 24, saboda zargin sama da fadi da dukiyar al'uma.

An tsare 'Yansanda uku suna dakon shari'a kan zargin wannan fallasar.

A cikin watan nan, wani kasidun ko bayanai na shugaban kasa kan kudurin karawa sojoji da aka tura yankin kasar na masu magana da harshen turancin sarauniya alawus. An nemi jami'an ma'aikatar tsaron kasar su biyu su bayyana domin amsa tambayoyi.

Kungiyoyin kare hakkin Bil'Adama sun juma suna sukar gwamnatin kamaru, dama na wasu kasashen Afirka a zaman wadanda basa gudanar da ayykansu a fili domin 'yan kasa su sani.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG