An Gano Gawarwakin Bakin Haure 27 Kusa Da Kan Iyakar Kasar Tunisiya

Wasu Bakin Haure

Hukumomin Libya sun ce akalla bakin haure 27 daga kasashen kudu da hamadar Sahara sun mutu a cikin 'yan kwanakin nan a cikin hamadar yammacin kasar da ke kusa da kan iyaka da Tunisia.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Libya ta wallafa a shafin Facebook, ta ce da yammacin Talata ne aka gano gawarwakin a kusa da kan iyaka kuma an tura wata tawagar bincike zuwa yankin. A cikin sakon, ma'aikatar ta wallafa hotunan bakin haure 'yan Afirka da ke karbar magani daga kungiyoyin likitocin Libya.

Mohammed Hamouda, mai magana da yawun gwamnatin Libya, ya tabbatar wa kamfanin dillacin Labarai na Associated Press gano gawarwakin sai dai ya ki bayar da karin bayani.

A watannin baya-bayan nan ne jami'an tsaron kasar Tunusiya suka fara kwashe wasu bakin haure daga yankunan gabar tekun kasar, tare da awon gaba da su zuwa wasu wurare daban-daban, kuma kamar yadda 'yan ciranin suka ce, suna jefar da wasu daga cikinsu a cikin hamada.

Gabashin gabar tekun Tunisiya ya mamaye makwabciyarta Libya a matsayin babban wurin kaddamar da bakin haure a yankin, galibi daga kasashen kudu da hamadar sahara, dake kokarin shiga Italiya da wasu sassan Turai cikin kananan jiragen ruwa.

Kwamitin kare hakkin bil adama na kasa a Libya, wata kungiyar kare hakkin gida da ke aiki da hukumomin Libya, ta ce ta yi amanna cewa jami’an tsaron Tunusiya sun kori bakin hauren da karfin tsiya ne, inda suka yi watsi da su a cikin sahara ba tare da ko ruwa ko abinci ba.

Ahmed Hamza, shugaban kwamitin, ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AP cewa jami'an tsaron kan iyakar Libya ne suka gano gawarwakin a ranar Talatar da ta gabata.

Sai dai mai magana da yawun rundunar sojin Libiya ya musanta cewa an gano gawarwakin mutane a kusa da kan iyakar Tunisiya a ranar Talata, amma ya ki yin karin bayani.

A wani lamari na daban kuma a jiya Laraba, ana kyautata zaton cewa bakin haure 41 ne suka nutse bayan da kwale-kwalen da ke dauke da su ya kife a gabar tekun Tunisiya.

Masu fataucin bil adama sun ci gajiyar rashin zaman lafiya na shekaru goma na Libya, suna samun wadata ta hanyoyin fasa kwauri na kasa da kasa.

~ AP