A cikin jawabinsa, shugaba Donald Trump ya bayyana cewa, “Wadannan shugabanni masu hangen nesa za su saka hannu kan jarjeniyoyi biyu na farko tsakanin Israila da kasashen Larabawa a cikin fiye da kashi ‘daya cikin hudu na karni,” a cewar Trump, ya kuma kara da cewa, “a tarihin Israila baki daya irin wadannan yarjeniyoyi biyu aka taba samu, yanzu kuma mun cimma nasarar biyu a cikin wata guda kacal.”
Firaministan Isira’ila Benjamin Netanyahu da Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa, Abdullah bin Zayed, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar da ake wa lakabi da “Abraham Accord”, ma’ana yarjajjeniyar girmama Annabi Ibrahim, uban Yahudu da Larabawa.
An fara cimma yarjajjeniya tsakanin Isira’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa ne ranar 13 ga watan Agusta, sai kuma ranar Juma’ar da ta gabata, ita ma kasar Bahrain ta ce a hukumance za ta amince da kasar ta Yahuduwa a matsayin kasa.