An Fara Taron Karfafa Dangantaka Tsakanin Jami'an Tsaro Da Matasa a Nijer

Kwararru da masharhanta sun ce taron zai taimaka wajen karfafa zaman lafiyar al'uma da kuma inganta dangantaka tsakanin jami'an tsaro da matasa.

Wasu cibiyoyin nazari a Nijer da ke bincike akan sha’anin tsaro sun fara gudanar da wani taro domin tattauna hanyoyin karfafa dangantaka a tsakanin jami’an tsaro da matasan kasar a ci gaba da neman hanyoyin magance matsalar tsaron da ta addabi al’uma.

Lura da irin koma bayan da rashin fahimta tsakanin matasa da jami’an tsaro ka iya haddasa sha’anin tsaro a wannan lokaci na yawaitar ayyukan ‘yan bindiga a kasashen yankin Sahel irinsu jamhuriyar Nijer, ya sa cibiyar DCAF mai nazari da bincike akan sha’anin tsaro da ke da ofishi a Geneva da cibiyar nazari da bincike akan dabarun samar da tsaro da ke karkashin fadar shugaban Nijer wato CNESS, shirya wannan taro don kara wa matasa farar hula da jami’an tsaro ilimi akan maganar kyautata cudanya inji jami’i a cibiyar DCAF Massaoudou Ibrahim.

A daya bangaren, taron wata hanya ce ta musayar dabarun aiki a tsakanin bangarorin kula da sha’anin tsaro. Abdoul Azizou Garba, shi ne mataimakin daraktan cibiyar CNESS, ya bayyana cewa ana samun ci gaba a duniya kuma akwai bukatar a samar da bayanai, dalili kenan aka shirya taron don kara wa juna sani da kuma karfafa dangantaka mai kyau tsakanin jami’an tsaro da manoma.

Ranar Alhamis 3 ga watan Disamba za a kammala taron, wanda kasar Jamus da kungiyar ECOWAS suka dauki dawainiyarsa, kwararru sun ce taron zai taimaka wajen karfafa zaman lafiyar al'uma.

Ga Souley Moumouni Barma da cikakken rahoton ta sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

An Fara Taron Karfafa Dangantaka Tsakanin Jami'an Tsaro Da Matasa a Nijer