An Fara Samun Musayar Ra'ayoyi Akan Zaben Michael Obi

Sanarwar da ministan matasa da wasanni Barrister Solomon Dalung yayi cewa shahararren dan wasan kwallon kafar nan Michael Obi shine kyaftin din ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya super Eagles dake shirye shiryen zuwa wasannin motsa jiki na Olympic na Rio, da za’a gudanar a kasar Brazil ta haifar da cece-kuce.

Tsohon mai Magana da yawun kwamitin wasannin motsa jiki na Olympic Tony Nezianya wanda ya sauka kwanannan ya bayyana ra’ayinsa akan zaben da aka yiwa dan wasan cewa bashi da kwarewa a kan harkokin wasannin motsa jiki na Olympic, dan haka bai can-canta ba.

Ya kara da cewa lamarin ya kashe mai gwiwa kwarai, domin kama yayi a barshi ya cigaba da buga wasan da ya saba yunda sabon shiga ne a cikin harkokin wasannin motsa jiki irin na Olympics, a maimakon ma a dauki gogagge wanda ya saba da wasannin Segun Toriola wanda yayi suna a wasannin motsa jiki na nahiyar Afirka.

Sai dai bai yi Karin haske akan cewa ko ministan ne ya kamata ya zabi kaftin din ‘yan wasan kokuma kwamitin dake kula da harkokin wasannin motsa jikin ba.