An Fara Taron Jami'an Kwastam Na Afirka Ta Yamma Da Tsakiya A Nijar

Lokacin taron Jami’an Kwastam na kasashen Afirka ta Yamma da Afrika ta Tsakiya Tsaki a Nijar

Jami’an hukumomin shige da fice ko Douane daga kasashen Afirka ta Yamma da ta Tsakiya sun fara gudanar da taro a birnin Yamai da nufin bitar halin da ake ciki a sha’anin shige da ficen kaya a kan iyakokinsu da neman hanyoyin magance wasu matsaloli.

Taron dai na da manufar bullo da shawarwari a kan maganar saukaka musanya a tsakanin jami’ai da samar da sassauci a harkokin kasuwancin kasa da kasa, da yaki da fataucin haramtattun abubuwa da kuma ayyukan tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasashe.

Taron Jami’an Kwastam na kasashen Afirka ta Yamma da Afrika ta Tsakiya Tsaki a Nijar

Taron wanda ke gudana a karkashin hukumar Douanes ko kuma Kwastam ta Duniya WCO ko OMD lokaci na yin waiwaye kan shawarwarin da aka tsayar a taron kwararru da ya gudana ne a Bamako a watan Mayun da ya gabata a ci gaba da karfafa matakan zuba ido kan ayyukan shige da ficen kaya a yankin Afrika ta Yamma da ta Tsakiya.

Darektan ofishin tattara bayanai na reshen hukumar OMD a yankin Afirka ta tsakiya da yankin tafkin Chadi, Ibrahim Joly Ange Moly, ya bayyana muhimmancin hada gwiwa a tsakanin yankunan na Yammaci da Tsakiyar Afirka.

Ya ce hada gwiwa a wannan fanni abu ne da zai taimaka a murkushe matsalolin ta’addanci wadanda ka iya tsallakawa daga wannan iyaka zuwa waccan.

Taron Jami’an Kwastam na kasashen Afirka ta Yamma da Afrika ta Tsakiya Tsaki a Nijar

Ya bada misalin yadda akan fitar da ababen sayarwa daga wannan yanki zuwa wancan, da yadda ‘yan ta’adda na iya amfani da wannan hanya don shigar da kayayyakin da za su cutar da jama’a, saboda haka, a cewarsa, hada gwiwa a tsakanin yankunan biyu na da muhimmanci.

Mataimakin shugaban kwamitin hadin gwiwar hukumomin Douanes na yankin Afrika ta Yamma da ta Tsakiya, kuma shugaban hukumar Douanes ta kasar Mali Amadou Konate wanda ya fara da tunatar da mahalarta muhimman taron na 29, ya gargade su a kan bukatar su natsu domin bullo da shawarwarin da za su kara inganta sha’anin shige da ficen kaya a wannan lokaci da ana fuskantar barazanar tsaro.

Jami’an Kwastam na kasashen Afirka ta Yamma da Afrika ta Tsakiya Tsaki a Nijar

Dilallan shige da ficen kaya a tsakanin kasashe da suka halarci bikin bude taro a matsayin baki sun bayyana fatan ganin zaman ya kula da matsalolin da suke fama da su a kan iyakoki, a cewar sakataren kungiyarsu Habibou Gado.

A kowace shekara kwararru kan harkokin kwastam na wadanan kasashe na haduwa sau biyu don tattaunawa game da tafiyar ayyukansu.

Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ce za ta karbi bakuncin taron farko a shekarar 2025.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

An Fara Gudanar Da Taron Jami'an Kwastom Na Afrika Ta Yamma Da Ta Tsakiya A Nijar.MP3