A ci gaba da daukar matakan dankwafe yunkurin ‘yan ta’adda, jami’an tsaro a jamhuriyar Nijar sun gudanar da wani gagarumin aikin binciken motocin haya, wanda ya bada damar cafke direbobin tasi sama da 100 a birnin Yamai.
Cikinsu har da wadan da ake ganin sunada alaka da ‘yan ta’adda, wannan matakin ya gamsar da kungiyar direbobin tasi ta Syncotaxi.
A sakamakon wasu bayanan da aka fahimta daga hare haren ta’addanci, a farkon watan nan da muke ciki ya sa jami’an tsaro suka tsaurara bincike, wanda tashin farko ya shafi 'yan babura kafin daga nan matakin ya koma bangaren motocin haya musamman tasi.
Wannan shine lamarin da ya bada damar kama wasu masu fakewa da aikin tasi, don tafka ta’asa kamar yadda shugaban kungiyar direbobin tasi ta Syncotaxi Gamatche Mahamadou ya bayyana.
Hukumomi da al’umar jamhuriyar Nijar sun dukufa yanzu haka da shirye shiryen taron shuwagabannin kasashen Afirka, da kasar ke karbar bakoncinsu a farkon watan gobe.
Saboda haka jagororin direbobin tasi ke kara nuna bukatar ganin jami’an tsaro sun ci gaba da tsaurara matakai domin kare dukkan wani yunkurin ‘yan ta’adda.
A jajibirin karamar Sallar da ta gabata, jami’an tsaro sun yi nasarar cafke wasu mutane kimanin 5 a anguwar filin jirgin saman Yamai, dauke da wasu abubuwa masu fashewa wadanda dubunsu ta cika, bayan da aka bi diddigin hirarrakin da suka yi ta wayar tarho da wasu manyan ‘yan ta’addan dake kasar Barkina Faso.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5