Ganin yadda kasashen duniya ke tsaurara matakan mayar da Nijar saniyar ware ta hanyar jerin takunkumin da ta ke fama da su a sakamakon abubuwan da suka wakana tun daga ranar 26 ga Watan Yulin 2023, ya sa wasu kungiyoyin rukunonin al'ummar kasar hada kai da zummar yi wa gwamnatin rikon kwarya rakiya a ayyukan mayar da kasar kan tafarkin dimokradiyya, mafarin kafa wata hadaka mai sunan Dynamique Citoyenne Pour Une Transition Réussie (DCTR) wace tsohon jagoran kungiyar ma'aikatan kwadago ta CDTN Issoufou Sidibé ke shugabanta.
Kungiyoyin sun kudiri aniyar bin hanyoyin da zasu bada damar jan hakalin kungiyar ECOWAS ta canza matsayinta kan kasar tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar, inji Anda Garba.
Matasa na da rawar takawa a sabuwar tafiyar da aka sa gaba a halin yanzu a wannan kasa da ke kokarin kufce wa ‘yan mulkin mallaka, a saboda haka hadakar ke hangen zagaya jihohin kasar.
Matakin takaita al’amuran sufuri a tsakanin Nijar da kasashen Najeriya da Benin da ya shafi harkokin kasuwanci da jigila sosai, da tafiyar hawainiyar da ake fuskanta a fannin hada hadar kudade, da kuma karancin wutar lantarki na kadan daga cikin matsalolin da ake fuskanta a Nijar sakamakon takunkumin kungiyar CEDEAO, a saboda haka kungiyoyin rukunonin al’umma suka shiga yunkurin neman hanyoyin da za su taimaka a fita kunyar sabuwar tafiyar da kasa ta dauri aniyar yi.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5