A ranar Litinin aka koma fafatawa a gasar Premier League ta Ingila, mako daya bayan kammala gasar cin kofin duniya.
Arsenal za ta karbi bakuncin West Ham domin dorawa a inda ta tsaya kafin a fara gasar ta cin kofin duniya a Qatar wacce Argentina ta lashe bayan da doke Faransa da ci 4-2 a bugun fenariti.
Arsenal ce dai take saman teburin gasar ta Premier da maki 37 inda Manchester City ke biye da ita da maki 32 sai Newcastle da maki 30.
Sai dai ana fargabar za ta iya fuskantar kalubale saboda rashin dan wasanta Gabriel Jesus da yake jinya.
A gasar cin kofin duniya Jesus wanda dan asalin kasar Brazil ne ya samu rauni a kwaurinsa.
A nata bangaren, West Ham kokari za ta yi ta kaucewa komawa rukunin ‘yan dagaji yayin da take matsayi na 16 a teburin gasar.
West Ham ta lashe wasanninta hudu cikin 15 da ta buga tun da aka fara wannan kakar wasa.