Lahadin nan ake fafata wasannin karshe na gasar Premier ta bana, wadda rana ce da kungiyoyi da dama za su san matsayinsu, ciki har da wanda zai lashe gasar.
A yayin da tuni aka san zakarun sauran gasannin league na Turai, wasu ma har sun daga kofi, gasar ta Premier ta bana kam za ta dau fasali ne a ranar karshe, inda za’a tantance zakara tsakanin mai rike da kambin, Manchester City da kuma Liverpool, wadanda su ne ke cikin takarar lashe kofin a halin yanzu.
Manchester City ce ke saman teburin gasar da maki 90, yayin da Liverpool take binta da maki 89, wato bambancin maki daya ta kenan a tsakaninsu.
Hakan na nufin ko wacce daga cikinsu na bukatar nasara a wasanta na karshe, tare da fatar dayan ta sha kashi domin ta daga kofin na bana.
A fafutukar karkare kakar wasanni a cikin kungiyoyi 4 na saman tebur kuma, tuni da Chelsea ta sami tabbacin karewa a ta 3 ko da kuwa ta sha kashi a wasanta na karshe da Watford, har sai idan Tottenham ta iya yin galaba kan Norwich da a kalla ci 18-0.
To sai dai Tottenham din ma na da jan aiki a gaban ta na tsare matsayin ta na 4 a tebur, domin kuwa Arsenal na dafe da keyarta tare da banbancin maki 2 kacal a tsakaninsu.
A can kasa kuma tuni da Watford da Norwich suka sami tabbacin faduwa daga gasar ta Premier, a yayin da cikon ta ukunsu za ta bayyana a gobe Lahadi tsakanin Burnley da Leeds United, da ke da maki maki 35 kowaccensu, amma Burnley ce a sama sakamakon yawan zura kwallaye.
Daga karshe dai kungiyar kwallon kafar PSG ta kasar Faransa ta sami nasarar ci gaba da rike shahararren dan wasanta Kylian Mbappe, duk kuwa da rahotannin da ke nuna cewa an cimma daidaito kan komawarsa kungiyar Real Madrid ta kasar Spain.
Mbappe dan kasar Faransa mai shekaru 23, ya yanke shawara tare da amincewa da zaben ci gaba da zama kungiyar ta shi, tare da rattaba hannu akan sabon kwantaragin shekara 3.
Ana sa ran kammala sa hannu kan sabuwar yarjejeniyar a yayin wasar karshe ta wannan kakar wasannin da kungiyar za ta buga da Metz, inda kuma ake sa ran za ta ba da sanarwa.
Tun a watan da ya gabata ne kungiyar ta PSG ta yi tayin biyan dan wasan zunzurutun kudi Yuro m.150 da sanya hannun kwantaragi, a kokarin da take yi na hana shi sauya gida.
Mbappe ya riga ya amince da biyan da Real Madrid ta taya masa domin komawarsa a can, to amma kuma ya sauya shawara.
Dan wasan gaba na kungiyar Manchester City ta Ingila, Kevin De Bruyne ya lashe lambar gwarzon dan kwallon gasar Premier na bana.
De Bruyne dan kasar Belgium mai shekaru 30, ya sami lambar ne bayan da ya sami mafi yawan kuri’u da aka tattara daga jama’a a shafin yanar gizo na gasar ta Premier, da kuma kuri’un da kaftin-kaftin na kungiyoyi da wasu kwararru a haujin kwallon kafa suka jefa.
Wannan ne karo na 2 da yake lashe kyautar, kasancewar ya taba samun lambar yabon a kakar wasanni ta 2019 da 2020, inda a yanzu ya bi sahun Thierry Henry, Cristiano Ronaldo da Nemanja Vidic, da suka taba lashe lambar fiye da sau daya.
Haka kuma takwaransa na kungiyar ta City, Phil Foden, shi kuma ya lashe lambar gwarzon matashin kwallo na gasar na shekara.
Foden ya kasance dan wasa na farko da ya taba lashe lambar sau biyu a jere a tarihi.
Saurari rahoton Murtala Sanyinna: