An Dawo Da 'Yan Najeriya Sama Da 160 Daga Libya

Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama a lokacin wata ziyara da ya kawo Amurka a bara

Kasar Libya dake fama da tashin hankali ta dawo da ‘yan Najeriya fiye da 160, dake zaune a kasar ba tare da izini ba, daga cikin su akwai mata 101 da kuma maza 60.

Wadannan dai sune ‘yan Najeriya, na farko da aka tasa keyarsu zuwa gida a wannan shekarar.

Hukumar ba da agajin gaggawa a Najeriya, watau NEMA, na ci gaba da karbar ‘yan Najeriyan, da ake dawowa da su daga kasar ta Libya.

Ko a jiya ma sai da hukumar ta NEMA, ta karbi ‘yan Najeriya, 161, da aka dawo da su daga Libyan, a cikin wadanda aka dawo da su har da kananan yara guda bakwai da jarirai biyu.

Dr. Abdullahi Onimode, ya ce hukumar ta NEMA, ta baiwa wadanda aka dawo da su kudade domin karasawa garuruwansu domin fara sabuwar rayuwa.

Ya kara da cewa dole ne a samar masu da wasu abubuwa da za su dogara da shi bayan dawowarsu gida.