Manyan batutuwan da aka tattauna a taron sun hada harda, amincewa da gudanar da zanga-zanga a matakin kananan hukumomin Nigeria, musamman a jihohin da har yanzu basu gudanar da zabe ba.
Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi a Najeriya, Kwamrad Ibrahim Khalid, yace za a gudanar da zanga zanga domin a gyara kundin tsarin mulki, wanda zai kai ga rusa tsarin da ya tanadi hukumomin zabe na jihohi don tabbatar da dorewar dimokaradiyya.
Shi kuma Barista Ahmed Sani, na ganin baiwa kananan hukumomi damar gudanar da zaben shugabanninsu zai kawo ci gaba a yankunan karkara. Yace wannan gwamnatin ta yi alkawarin barin kananan hukumomi su gudanar da zabensu, amma sai gashi yanzu suna bayyana cewa basu da kudin da zasu iya tabbatar da hakan.
Mallam Zakari Husaini Bura, yace sai an samar da wasu abubuwa uku idan har ana son kananan hukumomi su zamanto suna da ‘yancin kansu, na daya shine, a zabi shugabanni na gari, na biyu a sami Majalisa ta karamar hukuma, na uku shine samun kudi kaitsaye daga gwamnatin tarayya.
Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Mohammad.