An dakatar da dan wasan baya na Bournemouth da ake kira Tyrone Mings buga wasanni guda biyar a matsayin jan kunnen laifin taka dan wasan gaban Manchester United Zlatan Ibrahimovic.
Hukumar kwallo kafar ta zargi Mings da Ibrahimovic da aikata rashin da’a a ranar Litini a kana abin da ya faru a ranar Asabar a filin wasan Old Trafford inda kungiyoyin nasu suka yi kunnen doki.
Mings dai shine yasa kafa ya taka Ibrahimovic a ka, kafin daga bisani dan wasan na Manchester Ibrahimovic, ya mayar da martani da naushi.
Ibrahimovic dan asalin Sweden ya riga ya amince da laifinsa kuma ba zai yi wasanni uku ba, amma kungiyar Bournemouth, tana jayayya a kan wannan hukunci.
Duk da haka wata komishan mai zaman kanta ta samu Mings da aikata rashin da’a, kuma ba zai wasannin premier league guda biyar, da zasu hada da wadanda zasu yi da West Ham, Swansea, Southampton, da Liverpool da kuma Chelsea.
Your browser doesn’t support HTML5