A Yayin da gidan Rediyon muryar Amurka VOA ya cika shekaru 75 da kafuwa sashin Hausa na muryar Amurka, tare da hadin guiwar hukumar dake kula da kasashe masu tasowa ta Amurka USAID, sun shirya taro domin fadakar da jama'a illar cutar cizon sauro wadda aka yiwa lakabi da (kick malaria out) ga bil'adama Kamar yadda suka saba duk shekara inda suke kewaya jihohin tarayyar Najeriya.
A bana sashin Hausa na muryar Amurka zai gudanar da taronne a jihar Sokoto ta tarayyar Najeriya, a ranar talata 7/3/2017, kuma acikin shirin a kwai wasan kwallon kafa Kamar yadda aka saba duk shekara da za'ayi tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Sokoto Rima Academy, da kungiyar kwallon kafa ta VOA Flamingo Fc, dake garin Bauchi, a filin wasa na Giginya Memorial stadium, dake Sokoto a ranar talata 7/3/2017 da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya da Nijar.
Babban bako a wurin taron shine mai girma Kwamishinan lafiya na jihar Sokoto
Dr Balarabe Shehu Kakale.