Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta bada sanarwar daga ranar sake bude makarantu daga 1 ga watan Oktoba zuwa 15 ga wata, da nufin samun isasshen lokacin gyaran wuraren da za a yi amfani da su don tsugunar da mutanen da ambaliyar ruwa ta ruguza gidajensu.
Kawo yanzu an kiyasta cewa gidaje 32,959 ne suka ruguje sanadiyyar ambaliyar ruwa a fadin kasar, lamarin da ya shafi mutane sama da 350,915 wadanda galibinsu suka nemi mafaka a makaratu daban daban, dalili kenan da hukumomi kasar suka yanke shawarar daga ranar komawa makarantu, a cewar kakakin gwamnatin Nijer, Minista Abdourahamane Zakaria yayin da yake shaida wa wakilin muryar Amurka ta wayar tarho.
Baya ga asarar gidaje da dukiyoyi, ruwan saman da ake tafkawa kamar da bakin kwarya a fadin kasar ya hallaka mutane sama da 70 tare da haddasa lalacewar dubban gonaki da mutuwar dimbin dabobi, lamarin da ya sa gwamnatin kasar bude wata gidauniya da nufin tattara dubban miliyoyin cfa don tallafawa al’ummar kasar da bala’in ya rutsa da su.
Saurari cikakken bayanin Souley Barma cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5