An Dage Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka Ta 2021

  • Murtala Sanyinna

Shugaban CAF Ahmad Ahmad

An dage fafata gasar kwallon kafa ta cin kofin nahiyar Afirka da aka tsara gudanarwa a badi a kasar Kamaru.

An tsara za’a gudanar da gasar ne a watannin Janairu da Fabrarirun shekarar 2021, to amma a yanzu an dage ta da shekara daya saboda annobar Coronavirus, a wani taron hukumar kwallon kafar Afirka ta CAF.

Shugaban hukumar ta CAF Ahmad Ahmad ya ce an dauki matakin daga gasar zuwa 2022 ne saboda “hukumar ta na ba da muhimmancin gaske akan tsaron lafiyar al’umma.”

Sauran gasannin nahiyoyin duniya da dama ne su ma aka dakatar da fafata su sakamakon annobar, da suka hada da gasar cin kofin nahiyar Turai da Copa America.