Turkiyya da Rasha sun cimma wata sabuwar matsaya kan shirin tsagaita wuta a Syria, kuma suna kan aiki dangane da yadda wannan matsaya za ta fara aiki a daren yau Laraba.
WASHINGTON, DC —
Kamfanin dillancin labaran Anadolu na Turkiyya ya ruwaito cewa, wannan sabon tsari na da zimmar fadada shirin tsagaita wutar har zuwa birnin Aleppo, sai dai ba zai hada har da kungiyoyin ‘yan ta’adda ba.
Amma kuma Firai ministan Turkiyya, ya ce hukumomin Ankara ba su sauya matsayarsu kan cewa Shugaba Bashar al Assad ba zai sauka a mulki ba.
A makon da ya gabata, Rasha da da Iran da Turkiyya suka amince da wani kuduri, wanda ya shata yadda za a cimma matsaya wajen shawo kan rikicin na Syria.
Shugaban Rasha Vladimri Putin ya kuma ce kasashen sun amince za su hadu a Astana, babban birnin Kazakhstan domin ci gaba da neman bakin zaren wannan rikici na Syria.