Rasuwar Fisher na zuwa ne kwanaki hudu bayan da ta yanke jiki ta fadi a cikin jirgi, a lokacin ta na kan hanyar ta dawowa Amurka daga London.
Fisher wacce likitoci suka ce ta yi fama ne da matsalar bugun zuciya, ta rasu da safiyar yau Talata.
Labarin mutuwarta, ya karade kafofin yada labaran Amurka.
Ita dai Fisher ta fara fitowa idon duniya ne a shekarar 1975 a fim din “Shampoo.”
Rahotannin sun nuna cewa Fisher ta yanke jiki ne minti 15 kafin jirginsu ya sauka a birnin Los Angeles a makon da ya gabata.