Masu gabatar da shari’ar sun ce mutanen da ake tuhuma a shari’ar da ake yi a birnin Istanbul, sun taimakawa juyin mulkin kasancewar sun yi watsi da alhakin da ya rataya a wuyansu na kare shugaban kasa Recep Tayyip Erdogan.
Ashirin da daya daga cikin jami’an da ake zargi za su fuskanci zaman wakafi na din din din, idan har kotu ta same su da laifin kokarin hanbarar da gwamnati. Haka kuma sauran za su fuskanci zaman wakafi har na tsawon shekaru 15, idan aka same su da laifin hannu a wata kungiyar ta’addaci.
Turkiyya tana dora alhakin juyin mulkin kan Malam Fethullah Gulen, malamin da ke zaune yanzu haka anan Amurka, wanda ya musanta cewa yana da hannu a ciki. Masu sukar lamarin, ciki har da gwamnatocin Kasashen Yammaci da kungiyoyin kare hakkin bil Adama.
Wanda suka bayyana damuwa da cewa, ana wuce gona da iri wajen neman masu hannu a juyin mulkin, tare da fakon kungiyoyin da ke adawa da kudurorin gwamnatin shugaba Erdogan. Wanda hakan tamkar fakewa ne da guzuma don harbin karsana.