An Cimma Matsayar Tsagaita Wuta a Libya

Birnin Sirte a Libya, 18 ga watan Augusta, 2020.

Gwamnatin Libya da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya, ta ayyana shirin tsagaita-wuta a duk fadin kasar, ta kuma yi kira da a dakatar da duk wasu ayyukan soji a birnin Sirte - matakin da majalisar dokokin bangaren ‘yan adawa ta amince da shi.

Akwai dai yiwuwar wannan shiri na tsagaita-wuta ya samar da maslaha kan rikicin siyasar kasar, bayan da kasashen duniya suka nuna fargabar barkewar wani sabon rikici, yayin da bangarorin da ke takaddama da juna suke daura damarar wani sabon yaki kan birnin Sirte mai tashoshin da ake fitar da man fetur zuwa kasashen ketare.

Tun a watan Janairu wannan birni yake hannun dakarun da ke goyon bayan Khalifa Haftar.

Libya ta tsunduma cikin rudani ne tun bayan wani bore da kungiyar tsaro ta NATO ta marawa baya, wanda ya auku a shekarar 2011 - boren da ya yi sanadin hambarar da gwamnatin Moammar Gadhafi, wanda daga baya aka kashe shi.

Tun daga lokacin aka raba kasar biyu tsakanin wadanda ke gabashi da kuma yammaci, wadanda kowanensu na da dakaru da kasashen waje da ke mara musu baya.