KADUNA, NIGERIA - Muryar Amurka ta samu duba halin da al’ummar Tudun Birin ke ciki bayan kammala addu'ar kwana 40 da kai harin jirgin sojan Najeriya a garin.
'Yan uwa da abokan arzikin wadanda harin bom din ya hallaka da dama ne dai su ka halarci taron addu'ar arba'in da aka yi a garin na Tudun Biri.
Sai dai duk da kukan jinkirin cika alkawurran gwamnatin, jagororin al’ummar Tudun Birin sun ce gwamnati na kokari. Manyan garin sun ce bayan share hanyar garin yanzu haka an haka tushen fara ginin asibiti a garin.
Dama dai tun farkon harin, masana harkon tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai-ritaya suka nuna yuwar cewa za a yi biris da daukar mataki a bangaren gwamnati kuma ya ce gashi dai yanzu bayan kwanaki arba'in ba wani abu ba ya canja.
Babban abun da aka fi sa ran al’ummar Tudun Biri za su samu cikin gaggawa shine tallafin kudin da aka tattara, to sai dai dama tun lokacin kaddamar da kwamiti kan harin, gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ce wasu alkawurran kudaden sai an bi sahun su.
Daya daga cikin abubuwan lura dai shine daukewar kafar jami'an da daina ganin baki a yankin da masana ke cewa,akwai bukatar zuba jami'an tsaro a yankin baki daya.
Saurari cikakken shirin daga Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5