An ci tarar kungiyar Manchester City fam dubu 120 (kwatankwcin naira miliya 120) bayan da Erling Haaland da wasu ‘yan wasan kungiyar suka mamaye alkalin wasa suna korafi saboda ya hana su wata dama ta zura kwallo a karawar da suka yi da Tottenham a gasar Premier League.
An dai tashi da ci 3-3 a wasan a filin Etihad.
Hukumar Kwallon kafar Ingila ta yanke hukuncin cewa City ba ta hana ‘yan wasanta “nuna dabi’a mara kyau ba” a lokacin da lamarin ya auku a ranar 3 ga watan Disamba.
An ga Haaland cikin fushi yana kalubalantar alkali Simon Hooper kan yadda ya hana City samun dama inda har ya ci gaba da korafi har zuwa karshen wasan.
Ya kuma shiga shafin sada zumunta ya nuna bacin ransa a lokacin da yake mayar da martani kan bidiyon yadda aka tsayar da wasan.