Jamia’an sabuwar gwamnatin sun ce tun ranar littini ne aka tsare Yakubu Badjie, tare da wasu jamia’ai 8, to amma sai dai ba a bayyana takamaimai menene lafin su ba.
Jameh, wanda ya mulki kasar tun daga shekarar 1994, sailin da ya karfi mulki ta juyin mulki ya kafa wannan hukumar, wadda tayi kaurin suna wajen tursasa wa jamaa, da azabtar dasu wani lokacin har su kashe muddin kana adawa da gwamnati.
Jameh dai ya fadi zabe ne a lokacin da ya sake yunkurin neman wani sabon waadin mulkin kasar a cikin watan December bara, kuma ko bayan faduwar tasa sai yaki ya sauka daga kan karagar mulki sai da aka matsa masa lamba, daga makwabtar kasar, da wasu mutane wanda hakan ya tilasta shi barin Banjul babban birnin kasar zuwa wata kasar waje domin neman mafaka.
Kasar ta Gambia wadda karamar kasa ce cikin kasashen yammacin Africa karkashin sabon shugaban ta Adama Barow, yayi alkawarin samar da kwamitin binciken take hakkin bil adama da a aka gudanar karkashin tsohuwar gwamnatin Yaya Jameh, kana kuma za a sake duka hursunonin siyasa.
Yanzu haka dai ya zabtare yawan ikon wannan hukumar tattara bayanan sirri, kuma ya sake mata suna yadda zata zama ta kasa baki daya.
Wannan kamun dai da gwamnatin tayi shine na farko tun sailin da aka fatattaki tsohon shugaban kasar Yaya Jameh wanda ya tafi kasar Equtorial Guinea inda ya samu mafaka.