An dora ma Hassan Ali Khaire alhakin karfafa gwamnatin tarayya ta Somaliya tare da maido da kwanciyar hankali a wannan kasa dake fama da farmakin ‘yan kishin islama da kuma rashin ruwan sama.
A yau Alhamis shugaba Mohammed Abdullahi Farmajo ya bayyana nadin a shafinsa na Twitter.
Khaire ya shafe shekaru biyu da rabi da suka shige yana rike da mukamin Darekta mai kula da Afirka na kamfanin man kasar a Britaniya mai suna Soma Oil & Gas. Daga 2011 zuwa 2014 kuma, shine darekta mai kula da yankin gabashin Afirka na Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasar Norway.
A shekarar 2013, gwamnatin Somaliya ta damkawa Khaire aikin binciko man fetur da gas a cikin tekun gabar Somaliya.
Khaire mai shekaru arba’in da wani abu, sabon shiga ne a harkokin siyasar Somaliya. Amma wadanda suka san shi sun yaba da iya maganarsa, suka kuma ce yana da dangantaka mai kyau da shugabannin yankunan kasar Somaliya.
Facebook Forum