Masana harkar tsaro a Najeriya suna kiran shugabannin tsaron kasar su yi murabus domin sun zubar da mutuncin kasar a idanun duniya.
Dr. Bawa Abdullahi Wase masani akan harkokin tsaro yace sojojin kasar sun baiwa kasar kunya tare da zubar da mutuncinta. An sa siyasa a aikin soja. An cusa kwamandojin askarawan kasar cikin siyasa dalili ke nan yanzu ana aron bakunansu a ci masu albasa.
Idan da shugabannin hukumomin tsaro sojojin kwarai ne tunda aka sanar cewa ba zasu iya tabbatar da tsaro ba lokacin zabe to da sun yi murabus. Idan kuma basu yi ba kuma shugabancin kasar da gaske yake ya gudanar da zabe mai inganci da an sallami sojojin daga mukamansu. Kowanensu yayi rantsuwa cewa zai kare kasar ba tare da la'akari da ban bancin addin ba ko yare ko bangaranci ko ba. Yanzu abun da kwamandojin suka fada cin amanar kasa ne.
Ana kira ga 'yan hamayya kada su tada hankalin jama'a kada ya zama gwamnati nasar domin wanda ke kan mulki yanzu sun gane cewa babu tabbas idan an yi zabe zasu fadi.
Wasu kuma sun kwatanta matakin da jami'an tsaro suka dauka da juyin mulki to amma sun ce matakin ba zai razanasu ba. Abun da ba'a yi cikin shekaru hudu ba, ta yaya za'a iya yin shi cikin makonni shida. Lamarin yaudara ce kawai.
To saidai wasu na shirin garzayawa kotu domin sun ce shugaban INEC da jami'an tsaro basu da ikon daga zabe sai dai majalisun tarayya.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5