An Bukaci Giuliani Ya Mika Takardu Kan Ukraine

‘Yan jam’iyyar Democrat a majalisar wakilan Amurka sun turawa lauyan shugaban Amurka Donald Trump na kansa, Rudy Giuliani takardar gayyata kan wasu takardu da suka shafi kasar Ukraine, yayin da suke ci gaba da bincike kan tsige shugaban.

A jiya Litinin kwamitin da ke kula da bayanan sirri da na leken asirai, da kuma mai kula da harkokin waje a majalisar wakilan Amurka, suka bayyana aikawa da takardar gayyatar ga Giuliani tare da neman wasu banayan daga wasu abokanan huldarsa uku.

Da safiyar jiya Litinin din ne, a jerin wasu sakonni ta kafar Twitter, Shugaba Trump ya caccaki ‘yan jam’iyyar ta Democrat wadanda suka kaddamar da binciken da mai yiwuwa ya kai ga tsige shi, saboda korafin da wani mai kwarmata bayanan sirri ya gabatar.

Shi dai mai kwarmata bayanan, ya zargi Shugaba Trump da neman taimakon Shugaban Ukraine Zelenskiy wajen bankado wata badakala da ake zargin ta shafi dan tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, wato Hunter Biden, da nufin a bata mai suna don kada ya samu tikitin jam’iyyar Democrat, wajen tsayawa takarar shugaban kasa.