Shugaban Majalisar Dokokin Nijar Useni Pinni shi ne yayi jawabi akan makasudin taron na majalisar na shekara shekara.
A lokacin taron ne wakilan al'ummar kasar ke nazarin kasafin kudi da gwamnati ta sa a gabansu domin tantance kason da aka kebe wa kowane fanni na jin dadin rayuwar 'yan kasa.
Saidai sabanin yadda abun yake a shekarun baya a wannan karon ba'a bayyana adaddin kundin da tsarin ke kunshe dashi ba.
Onarebul Iro Sani shi ne mataimakin shugaban majalisar dokokin kasa. Abubuwan da suke cikin kasafin kudin sun hada da tabbatar da tsaron kasa wanda shi ne kan gaba. Za'a shirya yadda za'a yaki ta'adanci a kawar da 'yan ta'ada daga kasar Nijar domin kowane dan kasa ya kwanta lafiya da walwala koina yake.
Bayan samar da tsaro sai yadda kowa zai yi rayuwa cikin dadi. Za'a tabbatar abinci ya wadata cikin kasar. Bayan kawar da yunwa sai bada ilimi ga 'yan kasa. Za'a kuma maida hankali akan kiwon lafiya.
Kakakin gwamnati Asumana Malam Isa ya bayyana yadda gwamnati zata samu kudin da zata gudanar da ayyukanta. Yace kashi ukku cikin biyar zasu samu cikin gida. Masu hannu da shuni ne zasu kawo sauran kudin. Yace faduwar farashin fetur da yurenium da nera ta shafesu matuka.
To saidai dan majalisa na fannin 'yan adawa Lawali Ibrahim ya bukaci gwamnati ta dauki matakan da zasu sa talakawa su gani a kasa, musamman mutanen karkara.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5