Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Dabbobi Na Kara Kashe Mutane A Nijar


Kasuwar Dabbobi
Kasuwar Dabbobi

Watan jiya jami'an kiwon lafiya na dabbobi da mutane suka sanar da bullar cutar dabbobi wadda a lokacin ta hallaka mutane 25 da basu san cutar ce take damunsu ba.

Jiya ofishin kiwon lafiya na kasar Nijar ya sake fitar da wata sanarwa da ta tabbatar da yaduwar cutar dabbobi da ta kara kashe mutane a yankin Tawa.

Kawo yanzu an samu mutane tamanin da bakwai da suka kamu da cutar. Cikinsu ishirin da bakwai sun rigamu gidan gaskiya sabanin makon jiya inda mutane arba'in da ukku ne aka gano sun kamu da cutar kana ishirin da biyar suka kwanta dama.

Yaki da cutar da wasu cututuka dabbobi a Nijar
Yaki da cutar da wasu cututuka dabbobi a Nijar

Sanarwar tace dalilin cutar ce aka samu karuwar wadanda suka rasu saboda koda aka kaisu asibitoci rashin lafiyarsu ya tsananta basu iya rayuwa ba.Akan haka ne ofishin kiwon lafiya ya kara kira ga al'ummar kasar da su kiyaye matakan riga kafi game da cutar. Matakan kuwa sun hada da daina shan nonon dabbar da ta kamu da cutar ba tare da dafashi ba ko kuma cin naman da bai dahuba sosai. Haka kuma muamala da dabbar da ta kamu da ciwon nada illa ga mutum.

An gargadi duk wanda yake jin zazzabi ya je asibiti cikin gaggawa kada ya bata lokaci saboda akwai maganin ciwon idan an je asibiti da wuri.

Dangane da dabbobi kuma kamar saniya idan ta kamu da ciwon zata yi bari ko kuma ta dinga zawo har ta mutu idan bata samu kula ba. Kamata yayi a shaidawa likitocin dabbobi cikin gaggawa su duba idan cutar ce su bada magani.

Ga rahoton Haruna Mamman da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

XS
SM
MD
LG