Tun can baya hukumar zabe ta kuduri anniyar shirya zabukan a watan Janairu na shekara mai zuwa, wato shekarar 2017.
Shugaban jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulkin kasar Bazun Muhammad yayi karin bayani akan dalilan da suka sa suka yanke shawarar dage zabukan. Yace yadda aka gabatar da zaben da ya gabata akwai jam'iyyun da suka ce basu gamsu ba saboda wai katunan da aka yi zabe dasu basu da hotunan wadanda suka mallakesu. Tana yiwuwa mutum yayi anfani da kowane kati yace nashi ne. Idan kuma aka yi zabe akan hakan, wato yin anfani da katunan da basu da hotuna ana iya zargin gwamnati da yin magudi.
Wani abun kuma da taron ya lura dashi shi ne rashin shirin wasu jam'iyyu dangane da zabukan dake zuwa.Baicin haka ita ma kasar tana cikin wahalar rashin kudi.
Saidai 'yan adawa wadanda basu kasance a taron ba sun yi watsi da matakin da taron ya dauka a matsayin abun da ya sabawa doka. 'Yan adawa sun ce sun rubuta duk abubuwan da suka gani basu dace ba a zaben baya kuma sun kira a gyarasu kafin su kasance wurin taron amma ba'a yi ba. Dage zaben, inji 'yan adawa, ya sabawa doka.
Amma tuni mahukuntan kasar suka kafa kwamitin da zai aiwatar da shawarwarin da taron ya bayar duk da korafin 'yan adawa.
Saidai akwai ayar tambaya akan makoman kansiloli da shugabannin kananan hukumomi dake ci yanzu. Za'a rusasu ne ko za'a bari su cgaba da rike mukamansu bisa ga dokar da majalisar dokoki zata yi? Yanzu dai gwamnati tace zata kai shawara majalisar dokoki.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.