An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Hon Dogara Unity Cup A Jihar Bauchi

A jiya Lahadi 11 Fabarairu 2018, aka bude gasar kwallon Kafa wadda mai girma kakakin majalisar tarayyar Najeriya Rt Hon Yakubu Dogara ya dauki nauyin yi a fadin jihar Bauchi na kananan hukumomi a karkashin shirin da ake wa taken (Dogara Unity Cup 2018 karo na farko).

An bude gasar ne a filin wasa na Games Village, dake cikin garin Bauchi bisa jagoran shugaban Kwamintin wasanni na majalisar tarayyar Najeriya, Hon Bukar Goni Lawal, dan majalisa mai wakintar Yobe, a majalisar tarayya Abuja, ne ya bude gasar.

Babban bako Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar Da Sarkin Bauchi Dr Rilwanu Sulaima Adamu da Sarkin Dass Alh Usman Bilyamunu Usman, da kuma bako na musamman Coordinator Flying Eagles of Nigeria Abdulrahman Umar Baba sun sami wakilci a wajan wasan.

An buga wasanne tsakanin Kungiyar kwallon Kafa ta Dogara Boys da kuma Bogoro Boi B. inda aka tashi a wasan Dogara Boys, ta samu nasara kwallo daya da nema.

Duk kungiyar da ta samu nasara akwai babbar kyauta daga Rt Hon Dogara

haka kuma za'a kawo manajojin ‘yan wasan kwallon Kafa domin zakulo hazikan ‘yan wasan da za'a iya tsallakawa dasu kasashe daban daban da kuma wasu manyan kungiyoyin kwallon Kafa da suke fadin kasar don ciyar da ‘yan wasan gaba.

Wasan zai dauki wata guda kafin a kammalashi karkashin kwamintin LOC na wasan Alh Balarabe Douglas, da Paul Landi Sakatare da kuma Habila Daniel.