An Bayyana Sunan Mutumin Nan Da Ya Saci Jirgin Sama A Jahar Washington

Jirgin Saman da aka sace

An bayyana mutumin nan da hukumomi suka ce ya saci wani jirgin saman fasinja a jihar Washington a ranar Juma’a da suna Richard Russell.

Dan shekaru 29 da haifuwa ma’aikaci shirya jakkukuna a cikin jirgi ne a kamfanin jiragen sama na Horizon Air. Hukumomi sun ce ya yi aiki a ranar Juama’a kuma an ga shi saye da rigar aiki, lokacin da zai je ya dauki babban jirgin kamfanin kuma ya tashi da shi.

Ana sa ran ya mutu ne a lokacin da jirgin ya fadi da shi a tsibirin Ketron mai tazarar kilomita 48 kudu da filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Takoma, inda ya tada wuta a cikin wani daji, lamarin da hukumomi suka kira da kisar kai.

Wani amini ga iyalan Russell ya karanto wata sanarwa daga iyalan a jiya Asabar, yana mai cewa suna cikin bakin ciki da jin wannan labari.

A jiya Asabar ne masu bincike na gwamnatin tarayya suka fara bincike a kan sata da kuma hadari da jirgin da ya faru da yammacin shekaranjiya Juma’a.