Daga karshe dai kwamitinda shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kafa domin ya bashi shawarwari kan taron kasa da ya ayyana ya mika rahotonsa kuma an fara aiwatar da shawarwari da ya bayar.
WASHINGTON, DC —
Duk da cewa 'yan Najeriya da kungiyoyi suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da halaccin wannan kwamiti, tuni wasu mutane da kungiyoyin daga bangarorin kasar suka bayyana goyon bayansu kan kudurin kwamitin.
Wani lauya mai zaman kansa, Yusha'u Waziri Mamman yace sashe na 17 da 19 da wasu sassa daban daban na tsarin mulkin kasa sun baiwa shugaban kasa ikon kafa irin wannan kwamiti idan har ya hakikance cewa hakan zai taimakawa ci gaban kasa da zaman lafiya.
Ga karin bayani.
A kokarinda gwamnatin tarayya tace take yi na inganta zamantakewa, za a zabi wakilai 492 wadanda zasu wakilci sassan Najeriya daban daban a babban taron kasa da za a yi. A cikin wannan adadi, shugaba Jonathan zai zabi wakilai 114.
Duk da cewa 'yan Najeriya da kungiyoyi suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da halaccin wannan kwamiti, tuni wasu mutane da kungiyoyin daga bangarorin kasar suka bayyana goyon bayansu kan kudurin kwamitin.
Wani lauya mai zaman kansa, Yusha'u Waziri Mamman yace sashe na 17 da 19 da wasu sassa daban daban na tsarin mulkin kasa sun baiwa shugaban kasa ikon kafa irin wannan kwamiti idan har ya hakikance cewa hakan zai taimakawa ci gaban kasa da zaman lafiya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5